A Kallah Mutum 20 Sun Mutu A Wani Hari A Kabul
Jul 24, 2017 05:50 UTC
Hukumomi lafiya a Afganistan sun ce mutum 24 takwas ne suka rasa rayukansu, kana wasu kimanin 40 suka raunana biyo bayan wani hari a birnin Kabul.
Bayanai daga kasar sun ce an kai harin a safiyar yau Litini da mota a kusa da gidan wani babban malamin 'yan shi'a na kabilar Hazara mai suna Mohammad Moqaqeq.
Harin dai na zuwa ne a yayin da 'yan kabilar ta Hazara ke shagulgulan zagayowar shekara guda da harin hari da aka kai kan wani jerin gwano 'yan kabilar a ranar 23 ga watan Yuli bara wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 84 da raunana wasu sama da 300.
Harin kuma shi ne farko da kungiyar IS ko kuma Da'esh ta dauki alhakin kaiwa kan 'yan kabilar ta Hazara.
Tags