Dariruwan Palastinawa Sun Gudanar Da Sallar Juma'a A Masallacin Aksa.
Bayan kwashe makuni uku na hana gudanar da sallar juma'a a masallacin Aksa, a wannan juma'a dariruwan Palastinawa sun gudanar da salla cikin yanayi na tsaro.
Kamfanin dillancin Labaran Fars ya nakalto majiyar Kudus na cewa duk da irin yarjejjeniyar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu, a wannan juma'a, mahukuntan haramcecciyar kasar Isra'ila sun dauki matakan tsaron na musaman a kewayen masallacin Aksa domin tsoron sake aukuwar boren Palastinawa a yayin da aka haramta musu gudanar da sallar juma'a a masallacin na Aksa.
Tashar Telbijin din HKI ta biyu ta ce duk da cewa an samu konciyar hankali a Masallacin Aksa kuma al'amura sun dawo kamar yadda suke a baya, amma har yanzu jami'an tsaron HKI na tsoron barkewar rikici da kuma boren Al'ummar Palastinu.
A cikin makuni uku na baya-bayan nan, birnin Kudus da gabar tekun jodan sun fuskanci rikici tsakanin al'ummar Patastinu da jami'an tsaron HKI, bayan da jami'an tsaron HKI suka killace masallacin na Aksa.
Daga ranar 14 zuwa 23 ga watan Yulin da ya gabata, jami'an tsaron HKI bisa umarnin Benjamin Netanyahu Piraministan HKI sun rife masallancin Aksa ga masu salla da kuma masu kai ziyara masallacin, bayan da aka bude shi kuma an snaya na'urorin bincike a dukkanin kofofinsa, lamarin da ya harzika Palastinawa da kuma Al'ummar musulinmi na Duniya, wanda hakan ya tilasta mahukuntan HKI tsire na'urorin daga masallacin.