Al-sisy: Ya Kamata Katar Ta Fahimci Damuwar Kasashen Tekun Pasha.
Aug 08, 2017 12:09 UTC
Kamfanin dillancin labarun Spotnik ya ambato shugaban kasar Masar yana cewa; Wajibi ne Kasar Katar ta fahimci damuwar da larabawa takun fasha su ke da shi a kanta.
Abdulfattaha al-sisy wanda ya ke magana ayayin ganawa da dan sakon kasar Kuwait kuma minstan harkokin waje, Sabah Khalid al-hamd, al-sabah.
Kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular larabawa, Masar, Bahrain, sun dauki matakin yanke alakar diplomasiyya da kasar Katar a ranar 5 ga watan Yuni bisa zarginta da su ke yi da taimakawa ta'addanci.
Bugu da kari, kasashen sun hana jiragen saman Katar bi ta sararin samaniyarsu, kamar kuma yadda Saudiyya ta rufe iyakar kasa da take tsakaninsu.
Tags