Dakarun Iraki Na Ci gaba da Yakar 'Yan Ta'addan IS
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i23398-dakarun_iraki_na_ci_gaba_da_yakar_'yan_ta'addan_is
Sojojin Iraki sun kusanto yankin Tal Afar a ci gaba da farmakin da suka kaddamar domin kwato yankunan karshe dake hannun 'yan ta'addan Da'esh.
(last modified 2018-08-22T11:30:34+00:00 )
Aug 21, 2017 11:16 UTC
  • Dakarun Iraki Na Ci gaba da Yakar 'Yan Ta'addan IS

Sojojin Iraki sun kusanto yankin Tal Afar a ci gaba da farmakin da suka kaddamar domin kwato yankunan karshe dake hannun 'yan ta'addan Da'esh.

Hadin gwiwar dakarun da ya kunshi na Amurka da 'yan sanda da sojijin sun kasu gida uku zuwa yankin na tal Afar dake arewacin kasar.

Kuma babban gurinsu shi ne yin kawayanwa yankin a cikin kankanin lokaci, ikamar yadda mayan kwamandojin rundinar suka sanarwa da kamfanin dilancin labaren AFP.

Wannan dai na zuwa ne wata guda bayan da dakarun na Iraki suka kwato yankin Mosul birni na biyu kuma na karshe dake zamen sansanin na 'yan ta'ddan a Iraki.