Shirin Kasar Qatar Na Karfafa Alaka Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
(last modified Fri, 25 Aug 2017 04:47:24 GMT )
Aug 25, 2017 04:47 UTC
  • Shirin Kasar Qatar Na Karfafa Alaka Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta bayyana cewa: Cikin gaggawa zata dauki matakin dawo da jakadarta zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran domin karfafa alaka a tsakanin kasashen biyu.

A wani bayani da ma'aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta fitar a jiya Alhamis yana dauke da cewa: Qatar zata dauki matakin hanzarta tura jakadarta zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da nufin karfafa alakar jakadanci a tsakanin kasashen biyu. Wannan mataki na Qatar ya zo ne bayan janye jakadarta daga kasar ta Iran yau tsawon watanni 20 sakamakon matsin lamba da take fuskanta daga mahukuntan kasar Saudiyya.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Qatar ta bayyana cewa: Tun bayan kakaba takunkumin zalunci kan kasarta da Masarautar Saudiyya da kawayenta suka yi, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ce kadai ta bai wa Qatar damar yin amfani da sararin samaniyarta wajen gudanar da zirga-zirgan jiragen sama tare da tallafawa al'ummar Qatar da dukkanin kayayyakin bukatu a fagen rayuwa musamman kayayyakin abinci.

Tun a ranar 5 ga watan Yunin wannan shekara ta 2017 da muke ciki ne kasar Saudiyya da kwayenta na kasashen Larabawa musamman Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain suka dauki matakin yanke alakar jakadanci ta kasar Qatar tare da killaceta ta sama da kasa da kuma ta ruwa bisa zargin rashin biyayya ga kasar Saudiyya da ta nada kanta a matsayin jagoran kasashen Larabawa.

A ranar 23 ga watan na Yuni; kasashen Saudiyya, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain sun gabatar da wasu jerin bukatu ga kasar Qatar kan matukar ta amince da su, to a shirye suke su dage mata tarin takunkumin da suka kakaba kanta. Daga cikin bukatun akwai batun cewa: Qatar da yanke alakar jakadanci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da kawo karshen duk wata alakarta da kungiyoyin gwagwarmayar yankin gabas ta tsakiya da suka hada da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Lebanon da kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinawa.

Mahukuntan Qatar sun yi watsi da bukatun kasashen na Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya tare da byyana su da cewa; bukatu ne da suka yi hannun riga da matakan hankali, kuma tsoma baki ne karara a harkokin cikin gidan kasarta. Har ila yau mahukuntan kasar Qatar sun jaddada cewa: Kungiyoyin gwagwarmaya na Lebanon da Palasdinu, kungiyoyi ne da suke kare kansu daga matakan wuce gona da irin makiya, kamar yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kasa ce mai girma da karfi a yankin gabas ta tsakiya da dukkanin kasashen yankin zasu amfana da ita. Hakika wannan matsayi na mahukuntan kasar Qatar yana matsayin rusa wani babban makirci ne na siyasar kasar Amurka na kokarin maida Jamhuriyar Musulunci ta Iran saniyar ware a yankin, tare da rusa bakar siyasar yahudawan Sahayoniyya ta kokarin rusa kungiyoyin gwagwarmayar yankin da suka zame mata kadangaren bakin tulu. 

A fili yake cewa: Rashin mika wuyar kasar Qatar ga bakar siyasar masarautar Saudiyya musamman a fagen yanke alaka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran lamari ne da zai kara karfin gwiwa wa sauran kasashen Larabawa irin su Oman da Kuwait da tuni suke adawa da duk wani matakin yin biyayya ga bakar siyasar mahukuntan Saudiyya ido rufe. Kamar yadda wannan mataki na Qatar yake matsayin tamkar rashe ne ke neman juyewa da mujiya, inda da kadan kadan Saudiyya ta kama hanyar zama saniyar ware a tsakanin kasashen yankin.