Ya Zuwa Yanzu Mahajjata Miliyon 1.4 Suka Isa Kasar Saudia
Ya zuwa yanzu mahajjata daga kasashen duniya daban-daban kimani miliyon daya da dubu 400 suka isa kasar saudia don ayyukan hajji na bana.
Presstv a nan tehran ta nakalto majiyar hukumar shige da fishe na kasar Saudia tana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa mahajjata 1,313,946 suka isa kasar ta tashar jiragen sama, sannan wasu 78,504 ta kasa, a yayinda wasu 12,477 suka isa kasar ta Ruwa.
Hukumar ta kara da cewa tana saran kafin a rufe tashoshin jiragen sama da jiragen ruwa sa kuma bodojin kasar yawan mahajjatan bana zai kai miliyon biyu.
Majiyar ta kara da cewa, a bana yawan mahajjata ya karu da kashi 33% idan an twatanta da shekaran da ta gabata.
Mahajjana kasar Iran fiye da dubu 80 suka isa kasar saudia ya zuwa yanzu. Iraniyawa basu sami damar zuwa hajji a shekarara da ta gabata ba, don rashin amincewar da gwamnatin kasar Iran tayi kan sharuddan da gwamnatin saudia ta shimfina masu.