Turkiyya : Mutane 34 Suka Mutu A Sabon Harin Ankara
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i2383-turkiyya_mutane_34_suka_mutu_a_sabon_harin_ankara
Hukumomi a kasar Turkiyya sun sanar cewa adadin mutanen da suka rasa rayukan su bayan fashewar wani bam mai karfi a tsakiyar Ankara babban birnin kasar sun kai 34.
(last modified 2018-08-22T11:27:58+00:00 )
Mar 14, 2016 06:30 UTC
  • hari a Ankara
    hari a Ankara

Hukumomi a kasar Turkiyya sun sanar cewa adadin mutanen da suka rasa rayukan su bayan fashewar wani bam mai karfi a tsakiyar Ankara babban birnin kasar sun kai 34.

Da yake bayana hakan ga manema labarai bayan wani taron tsaro na gwamnatin kasar, ministan lafiya na kasar Mehmet Muezzinoglu ya ce kawo yanzu adadin mutanen da suka rasu sun kai 34, sanan wasu 125 sun raunana a tashin bam din na jiyya Lahadi.

A hannu daya kuma ministan cikin gida na kasar Efkan Ala, ya bayana cewa an kai harin ne da wata karamar mota a kusa da wata tashar Bus a gundumar Kizilay, inda motoci da dama suka kone, koda yae wasu rahotanni sun ce an ji karar harbe-harben bindiga bayan fashewar bam din.

Ministan ya kara da cewa ana gudanar da bincike domin gano suwa keda hannu a wannan aika-aika kuma nan bada jimawa ba zasu sanar da sakamakon binciken, sannan a cewar sa kasar sa ba zata taba kasa a gwiwa ba akan yaki da ta'adanci.

kawo yanzu babu wata kungiya data dau alhakin kai harin.

Idan ana tune ko a watan da ya gabata ma an kai makamancin wannan harin a birnin na Ankara wanda ya salwantar da rayukan mutane kimanin 30, wanda

wata kungiyar 'yan tawayen Kurdawa ta dauki alhakin kaiwa.