Masar: Martanin "Yan'uwa Musulmi Akan Shirin Zaben Shugaban Kasa
(last modified Tue, 19 Sep 2017 12:25:03 GMT )
Sep 19, 2017 12:25 UTC
  • Masar: Martanin

Kungiyar ta 'yan'uwa musulmi ta ce ba za aminta da halarcin zaben da za a yi a cikin kasar ta Masar ba.

Kakakin kungiyar ta 'yan'uwa  Tal'at, Fahmy, ya ce; Duk wani zaben da za a gudanar a Masar kama daga na 'yan majalisa zuwa na shugaban kasa, matukar Muhammadu Mursi baya ciki, to ba shi da halarci.

Tal'at Fahmy ya kara da cewa; Muhammadu Mursi shine halartaccen shugaban kasar Masar, kuma bai mika ikon da yake da shi ba ga waninsa.

Wannan shi ne maida martani na farko da kungiyar 'yan uwa musulmi su ka yi dangane da shirye-shiryen zaben shugaban kasa da za a yi a shekara mai zuwa.

Tun a 2013 ne Abdulfattah al-Sisy ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da shugaba muhammadu Mursi daga kan mulki.