Siriya : Sojin Rasha Sun Hallaka 'yan Ta'addan (IS) 120
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i24725-siriya_sojin_rasha_sun_hallaka_'yan_ta'addan_(is)_120
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa dakarunta sun hallaka 'yan ta'addan da'esh 120 a wani harin sama da aka kai masu.
(last modified 2018-08-22T07:00:48+00:00 )
Oct 07, 2017 07:27 UTC
  • Siriya : Sojin Rasha Sun Hallaka 'yan Ta'addan (IS) 120

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa dakarunta sun hallaka 'yan ta'addan da'esh 120 a wani harin sama da aka kai masu.

Ko baya ga 'yan ta'addan sanarwar ta ce an hallaka wasu sojojin haya na kasashen ketare 60 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

Sanarwar ta kuma ce an tarwatsa wani sansanin 'yan ta'addan a gabashin yankin Mayadine, tare da hallaka wasu 'yan ta'addan kimanin 40 a kusa da birnin Abu Kamal.

Mayadine dai shi ne yanki na karshe da kungiyar 'yan ta'addan ta (IS) ko kuma Da'esh ke rike da a Siriya.