Jiragen Amurka Marar Direba Sun Hallaka 'Yan IS A Yemen
(last modified Tue, 17 Oct 2017 05:50:16 GMT )
Oct 17, 2017 05:50 UTC
  • Jiragen Amurka Marar Direba Sun Hallaka 'Yan IS A Yemen

Rundinar sojin Amurka ta sanar da hallaka gomman 'yan ta'addan Da'esh a wasu sansanoni biyu a kasar Yemen.

Wannan dai shi ne karon farko da Amurka ta yi amfani da jiragen sama marar direba don kai hari wa 'yan ta'addan a wannan kasar ta Yemen dake fama da rikici.

Amurka ta ce ta kai harin ne cibiyoyin atisayen 'yan ta'addan dake lardin Baida wanda ya hallaka da dama daga cikinsu.

Sanarwar da ofishin dake jagorantar ayyukan soji na Amurka a yankin ya fitar ya ce 'yan ta'addan na mafani da sansanonin ne don horar da mutanensu dake kai hare hare da makamai manyan da kanana.

A can baya dai Amurka na amfani da jigarenta marar matuka don kai hari kan reshen 'yan ta'addan Al-qaida a yankin kasashen larabawa (Aqpa), amman wannan shi ne karon farko da tayi amfani da su kan 'yan ta'addan IS ko kuma Da'esh a Yemen.