An Bude Sabon Zagayen Tattaunawa Kan Rikicin Siriya A Astana
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25253-an_bude_sabon_zagayen_tattaunawa_kan_rikicin_siriya_a_astana
Yau Litini an bude wani sabon zagayen tattaunawa kan rikicin kasar Siriya a birnin Astana na kasar Kazakstan.
(last modified 2018-08-22T07:00:55+00:00 )
Oct 30, 2017 13:52 UTC
  • An Bude Sabon Zagayen Tattaunawa Kan Rikicin Siriya A Astana

Yau Litini an bude wani sabon zagayen tattaunawa kan rikicin kasar Siriya a birnin Astana na kasar Kazakstan.

Wannan taron na kwanaki biyu na da manufar tattaunawa kan halin da ake ciki a kasar ta Siriya, a daidai lokacin da al'amuran jin kai ke kara dagulewa a wannan kasa.

Kasashen Rasha da Iran da kuma Turkiyya ne suka shirya taron, wanda shi ne irinsa na bakwai da ake yi.

Bangarorin dai sun cimma nasara samar da tuddan mun-tsira a yankuna da dama na Siriya.

Wakilin kasar Rasha a taron, Alexandre Lavrentiev, ya bayyanawa manema labarai cewa akwai yiyuwar samun mafitar siyasa a kasar ta Siriya.

Kafin hakan dai shugaba Bashar Al-assad na Siriyar dai ya bayyana cewa a shirye yake ya bi wannan hanya ta shirya zaben 'yan majalisar dokoki da kuma na shuagaban kasa.