Harin Da'esh Ya Kashe Fararen Hula Da Dama A Gabashin Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25325-harin_da'esh_ya_kashe_fararen_hula_da_dama_a_gabashin_siriya
Rahotanni daga Siriya na cewa daruruwan fararen hula ne suka gamu da ajalinsu a wani hari da 'yan ta'adda na kungiyar Da'esh suka kai da mota a wani sansaninsu dake gabasnin birnin Zer- Ezzor.
(last modified 2018-08-22T07:00:56+00:00 )
Nov 05, 2017 02:18 UTC
  • Harin Da'esh Ya Kashe Fararen Hula Da Dama A Gabashin Siriya

Rahotanni daga Siriya na cewa daruruwan fararen hula ne suka gamu da ajalinsu a wani hari da 'yan ta'adda na kungiyar Da'esh suka kai da mota a wani sansaninsu dake gabasnin birnin Zer- Ezzor.

Bayanai sun nuna cewa wata mota  ce ta tarwashe a kusa da wata babbar motar dakon mai a kusa da sansanin da ya kunshi iyalai masu yawa dake gujewa yakin da ake da 'yan kungiyar ta Da'esh a yankin.

Hukumar dake sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama a wannan kasa ta Siriya (OSDH) ta rawaito cewa, gomman mutanen da suke tsare zuwa yankin sun bata bayan bata.

Wannan dai shi ne hari irinsa na biyu a kasa da wata guda da ake kaiwa kan fararen hula dake gujewa yakin da ake da 'yan ta'addan na Da'esh.

Harin na jiya Asabar ya kuma zo ne kwanaki biyu bayan da sojojin Siriya da sauren bangarorin dake dafa masu baya suka kwace iko da birnin na Zer- Ezzor da kewayensa daga hannun 'yan kungiyar ta Da'esh.