An Kori Ministoci Da 'Ya 'Yan Sarauta A Saudiyya
Rahotanni daga Saudiyya na cewa an cafke wasu daga cikin 'ya yan masarautar kasar 11 da wasu gomman ministoci tsaffi da wadanda ke kan aiki, a wani lamari da aka bayyana ba'a taba ganin irinsa ba a wannan kasa.
Ko baya ga hakan a cewar tashar talabijin ta Al-Arabiya, an kori wasu manyan jami'an tsaron gardi tsarki da kuma na ruwa na kasar.
Bayanai daga kasar sun ce wannan matakin ya biyo bayan da masarutar kasar ta kafa wani kwamiti na yaki da cin hanci da rashawa da yarima mai jiran gado Mohammed ben Salmane ke jagoranta.
Saidai tuni masu sharhi suka fara danganta lamarin da yunkurin share fage na yariman mai jiran gado dan shekaru 32, wato Mohammed ben Salmane na nisanta kansa da duk wasu makusantansa masu adawa da manufofinsa, kafin mahaifinsa Sarki Salman ya mika masa sarautar kasar.
Wasu daga cikin masu sharhi sun ce dayewa daga cikin wadanda aka kora na adawa da siyasar yariman mai jiran gado, musamen kan batun maida Qatar saniyar ware da siyasarsa da wasu kasashen ketare da yunkurin saida wasu kamfanonin kasar kuma suke bakin aljihun gwamnati.
A watan Oktoba da ya gabata Mohammed Salman ya sanar da anniyarsa ta canza Saudiyya daga kasa mai tsatsauran ra'ayin addini na Wahabiyanci da ya kyankyasa mayakan jihadi a kasashen duniya da dama zuwa wata kasa mai sassaucin ra'ayi.