Lavrov: Ficewar Sojojin Rasha Daga Siriya, Don Karfafa Tattaunawar Sulhu Ne
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewar kasar Rasha ta janye wani bangare na sojojinta daga kasar Siriya ne don karfafa shirin tattaunawar sulhu da ake yi da nufin kawo karshen rikicin kasar cikin ruwan sanyi.
Kamfanin dillancin labaran Interfax na kasar Rashan ya bayyana cewar minista Lavrov ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai inda ya ce kasar Rasha ta dau matsayar janye wani bangare na sojojin nata daga kasar Siriya ne don kuwa sun gama aiwatar da aikin da aka tura su Siriyan don shi wanda shi ne raunana karfin 'yan ta'addan da suke kasar.
Ministan harkokin wajen Rashan ya kara da cewa a halin yanzu dai sojojin gwamnatin Siriya su ne suke rike da wajajen da a da 'yan ta'addan suke rike da su bayan gagaumar koma bayan da suka fuskanta sakamakon hare-haren da sojojin saman Rashan.
A shekaran jiya ne dai shugaban kasar Rashan Vladimir Putin, bayan tattaunawa da shugaban kasar Siriya Bashar al-Asad, ya ba wa ministan tsaron kasar umurnin fara janye wani bangare na sojojin kasar da suke Siriyan.