Saudiyya: An Kashe Sojan Saudiyya Guda A Yankin Katif
Nov 07, 2017 03:00 UTC
Tashar telbijin din al-akhbariyyah ta Saudiyya ta ce; An Kashe sojan ne a jiya litinin.
Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken bayani da jami'an gwamnatin ta Saudiyya suka bayar dangane da harin.
Yankin na Katif wanda mazaunansa mabiya mazhabar shi'a ne, sun dade suna fuskantar takurawa da matsi daga mahukuntan kasar ta Saudiyya.
A cikin watannin bayan nan Saudiyyar ta mayar da yankin tamkar barikin soja bayan da ta girke jami'an tsaro masu yawa. An kashe mazauna birnin da yawa tare da kame wasu masu yawa.
Tags