Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Tabbatar Da Sabani A Tsakanin Manbobin Kungiyar
Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya bayyana cewa akwai sabani a tsakanin kasashen larabawa musaman ma kan abinda ya shafi harakokin tsaro
Tashar telbijin din Aljazira ta nakalto babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Ahmad Abul-Gheit na cewa babu mahanga guda a tsakanin manbobin kungiyar kasashen larabawa musaman ma kan abinda ya shafi harakokin tsaron kasashen.
Ahmad Abul-Gheit ya bayyana fatansa a game da samun hadin kai a tsakanin kasashen larabawan musaman ma kan abinda ya shafi harakokin tsaron kasashen su.
A yayin da aka tambaye shi kan alakar da ake tsakanin kungiyarsu da Iran, Abul-Gheit ya ce kasashen larabawa nada kyakkyawar alaka da jumhoriyar musulinci ta Iran kuma kungiyar a shirye take ta hau tebirin tattaunawa da jumhoriyar musulinci ta iran domin samar da mahanga guda da ta hada bangarorin biyu.
Rikici tsakanin kasashe manbobin kungiyar hadin kan kasashen larabawa ya samo asali ne kan yadda wasu kasashe daga cikin su ke kokarin yiwas sauren milki mallaka, da hakan ke kokarin wargaza kungiyar.