Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Ta Tabbatar da Baraka A Cikinta
Dec 02, 2017 07:20 UTC
Babban sakataren kungiyar ta kasashen larabawa Ahmad Abul-Ghaid ne ya ce akwai sabani a tsakanin kasashen larabawa, musamman akan batun tsaro.
A jawabin da ya gabatar a birnin Rom a wajen taron kasashen da ke gabar ruwan Medtrenia, Ahmad Abul Ghaid ya bayyana cewa; A cikin kasashen larabawan da akwai mahanga daban-daban akan bai wa tsaronsu muhimmanci.
Abul Ghaidh ya yi fatan cewa batun tsaron zai zama wanda zai hada dukkanin kasashen larabawan wuri guda.
Babban sakataren kungiyar kasashen ta larabawa ya kuma ambato kyakkyawar alakar da take a tsakanin larabawa da Iran, kuma kungiyar tana son bude tattaunawa da jamhuriyar musulunci ta Iran wacce za ta kai ga fahimtar juna.
Tags