Shugaban Palasdinawa Ba Zai Gana Da Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Ba.
Ministan harkokin wajen Palasdinawa ne ya bayyana cewa Mahmud Abbas Abu Mazin ba zai gana da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence da zai kawo ziyara ba.
Minitsan harkokin wajen na Palasdinu ya ce; matakin na shugaban gwamnatin kwarya-kwaryar palasdinu yana a matsayin kin amincewa ne da matakin shugaban kasar Amurkan Donald Trump na amincewa da birnin Kudus, a mastayin babban birnin haramtacciyar Kasar Isra'ila.
Riyahd al-Maliky ya kuma kara da cewa; Babu wata alaka da za ta gudana a tsakanin Jami'an Amurka da kuma na Palsdinu.
A can kasar Masar ma shugaban cibiyar Azhar, sheikh Ahamd Khatib ya ki amincewa da ganawa da Mike Pence saboda kin yarda da matakin na shugaba Donald Ttump akan Kudus.
Shi ma shugaban Kiristocin Kibdawan Masar, papa Tawadros na 2 ya soke duk wata ganawa da jami'an na Amurka.