Ana Ci Gaba Da Gumurzu Tsakanin Palasdinawa Da Sojojin Gwamnatin H.K.Isra'ila
(last modified Tue, 12 Dec 2017 11:57:03 GMT )
Dec 12, 2017 11:57 UTC
  • Ana Ci Gaba Da Gumurzu Tsakanin Palasdinawa Da Sojojin Gwamnatin H.K.Isra'ila

Ana ci gaba da gumurzu mai tsanani tsakanin Palasdinawa da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a yankunan da suke gabar yammacin kogin Jordan.

Yau tsawon kwanaki ke nan ana ci gaba da dauki ba dadi tsakanin al'immar Palasdinu da suke yankunan gabar yammacin kogin Jordan da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sakamakon matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Wani sabon gumurzun ya kunno kai a safiyar yau Talata musamman a garuruwan Bait-Laham, Baitu-Uyun da Khalil, inda Palasdinawan suka ja daga tare da hana sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila samun damar kutsawa zuwa cikin yankunan na Palasdinawa.