Sojojin Gwmnatin H.K.Isra'ila Sun Tsaurara Matakan Tsaro A Yankunan Palasdinawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i26365-sojojin_gwmnatin_h.k.isra'ila_sun_tsaurara_matakan_tsaro_a_yankunan_palasdinawa
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun tsaurara matakan tsaro a yankunan Palasdinawa da suke mamaye da su a gabar yammacin kogin Jordan gami da mashigar Zirin Gaza.
(last modified 2018-08-22T11:31:08+00:00 )
Dec 15, 2017 12:15 UTC
  • Sojojin Gwmnatin H.K.Isra'ila Sun Tsaurara Matakan Tsaro A Yankunan Palasdinawa

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun tsaurara matakan tsaro a yankunan Palasdinawa da suke mamaye da su a gabar yammacin kogin Jordan gami da mashigar Zirin Gaza.

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tana jin tsoron Palasdinawa zasu gudanar da zanga-zanga mai tsanani a yau Juma'a domin nuna rashin amincewa da matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila; sakamakon haka ta jibge sojojinta a yankunan Palasdinawa da ta mamaye a gabar yammacin kogin Jordan da kuma mashigar yankin Zirin Gaza.

Har ila yau jami'an tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi kawanya wa birnin Qudus da nufin murkushe duk wata zanga-zangar Palasdinawa a yau Juma'a.