CacarBaki Tsakanin Sudan Da Masar Na Kara Tsananta
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i26773-cacarbaki_tsakanin_sudan_da_masar_na_kara_tsananta
Bayan ziyarar kwanaki uku da shugaban kasar Turkiya ya kai kasar Sudan ya kuma gana da shugaban kasar a Sudan Umar Hassan Al-Bashir jaridun kasar masar sun yi ca a kan wannan ziyarar sun kuma soki kasar Sudan kan mikawa kasar Turkiya tsibirin Swakan dake cikin tekun Maliya.
(last modified 2018-08-22T07:01:12+00:00 )
Dec 28, 2017 03:23 UTC
  • CacarBaki Tsakanin Sudan Da Masar Na Kara Tsananta

Bayan ziyarar kwanaki uku da shugaban kasar Turkiya ya kai kasar Sudan ya kuma gana da shugaban kasar a Sudan Umar Hassan Al-Bashir jaridun kasar masar sun yi ca a kan wannan ziyarar sun kuma soki kasar Sudan kan mikawa kasar Turkiya tsibirin Swakan dake cikin tekun Maliya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kafafen yada labarai na kasar Masar suna sukar gwamnatin kasar Sudan suna kuma ganin ta mikawa kasar Turkiya wannan tsibirin ne don fusata gwamnatin kasar Masar. 

Banda haka wasu kafafen yada labarai sun nuna cewa gwamnatin sudan ce take horar da yan ta'adda wadanda suke kai farmaki a kan kiristocin kasar ta Masar.

Wasu jaridun kasar Masar sun nakalto Abdul-Mahmood Abdul-Halim jakadan kasar Sudan a kasar Masar, a kuma kungiyar kasashen larabawa wacce cibiyarta take birnin Alkahira yana maida martani ga wadannan zarge-zarge inda yake cewa mafi yawan kafafen yada labaran da suka wannan zargin basu san abin da suke yi ba.