Palasdinu: Bapalasdine Guda Ya Yi Shahada A Yammacin Kogin Jordan
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27371-palasdinu_bapalasdine_guda_ya_yi_shahada_a_yammacin_kogin_jordan
Majiyar labarun Palasdinu ta ce Bapalasdinan ya yi shahada ne sanadiyyar harin da sojojin Sahayoniya suka kai wa garin Jenin a jiya Laraba da dare.
(last modified 2018-08-22T07:01:18+00:00 )
Jan 18, 2018 04:09 UTC
  • Palasdinu: Bapalasdine Guda Ya Yi Shahada A Yammacin Kogin Jordan

Majiyar labarun Palasdinu ta ce Bapalasdinan ya yi shahada ne sanadiyyar harin da sojojin Sahayoniya suka kai wa garin Jenin a jiya Laraba da dare.

Bugu da kari sojojin 'yan sahayoniyar sun yi awon gaba da wasu matasan palsdinawa daga garin na Jenin.

A gefe daya, tashar talabijin  din al-alam ta bada labarin cewa; an yi taho-mu-gama da makamai a tsakanin 'yan gwgawarmaya da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke Jenin.

Tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar Kasar Isra'ila, al'ummar palasdinu suka fara yin boren rashin amincewa.

Kawo ya zuwa yanzu adadin wadanda suka yi shahada a wannan boren sun kai 22, yayin da wasu da dama su ka jikkata.