Syria: Mayakan Kurdawa Sun Kama Sojojin Turkiya
Mayakan kungiyar Kurdawan Syria wacce aka fi sani da YPK sun sanar da kame sojojin Turkiya 16 a yau juma'a.
Mai magana da yawun mayakan Ahmad Shauki ne ya bada labarin kame sojojin Turkiya, da ya ce ya faru ne a yankin Jindires. Har ila yau Shauki ya kuma kara da cewa a yayin gumurzun da suka yi da sojojin na Turkiya 4 daga cikin mayakansu sun bace.
Wata majiyar ta kungiyar YPK ta ce; kungiyar tasu tana kare yankin Afrin ne daga hare-haren Da'esh, kuma yankin wani sashe ne na kasar Syria. Kurdawan sun zargi Turkiya da kokarin balle yankin daga karkashin Syria.
Tun a ranar asabar din da ta gabata ne dai Turkiya ta fara kai hari a yankin Afrin na kasar Syria domin kawar da abinda ta kira hatsarin 'yan ta'addar kungiyoyin Kurdawa.
Syria ta yi Allah wadai da harin na sojojin Turkiya tare da bayyan hakan a matsayin keta hurumin kasar syria