Kasashen Larabawa: Barazana Ga Quds Wasa Da Wuta Ne
Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Abulghaid ya bayyana cewa matsayin da gwamnatin kasar Amurka ta dauka baya-bayan nan kan birnin Quds Wasa da wuta ne.
Kamfanin dillancin Labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto babban sakataren yana bayyana haka ne a jiya Alhamis a lokacinda ya ke jagorantar taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar a birnin Alkahira na kasar Masar, inda cibiyar kungiyar ta kasashen Larabawa take.
A ranar 6 ga watan Decemban shekara ta 2017 da ta gabataa ce shugaban kasar Amurla Donal Trump ya bada sanarwan cewa ya amince da birnin Quds a matsayin cibiyar gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila. Ya kuma bawa ofishin jakadancin Amurka da ke Isra'ila ta fara shirye-shiryen maida ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin na Quds. Shugaban ya yi gaban kansa ya daukar wannan matakin duk tare da rashin amincewar kasashen yankin da kuma wasu kasashen duniya gaba daya.
Birnin Quds dai yana dauke da masallacin Al-Aqsa wacce ta kasance alkiblar musulumi ta Farko sannan yana daga cikin muhimman wurare masu tsarki ukku na musulmi. Yahudawan Isra'ila sun amamaye birnin tun yakin shekara ta 1967 M.