Labanon : Kurdawa Sun Yi Zanga-zanga Kan Farmakin Turkiyya
(last modified Mon, 05 Feb 2018 16:44:09 GMT )
Feb 05, 2018 16:44 UTC
  • Labanon : Kurdawa Sun Yi Zanga-zanga Kan Farmakin Turkiyya

A Labanon, daruruwan Kurdawa ne suka gudanar da wata zanga-zanga yau Litini gaban ofishin jakadancin Amurka dake Beirut, domin yin allawadai da farmakin da Turkiyya ke ci gaba da kaiwa a yankin Afrin na Siriya.

A baya baya nan dai ana gudanar da zanga-zanga a sassa daban na duniya kan farmakin da Turkiyya ta soma kaiwa tun a ranar 20 ga watan Janairu kan mayakan Kurdawa na (YPG).

Daya daga cikin masu zanga zangar mai suna Rida dan asalin yankin Afrin ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa '' mun murkushe mayakan IS da kuma rage karfin a duniya, amma yanzu kasashen duniya sun koma yakarmu.

Turkiyya dai na kallon mayakan Kurdawa na YPG a matsayin 'yan ta'adda, a yayin da kuma suke zaman kawayen Amurka wajen yaki da mayakan jihadi.

A wani labari kuma ma'aikatar harkokin wajen Iran, ta bukaci Turkiyya data kawo karshen farmakin da take kaiwa a yankin na Afrin, tare da jan kunnan Turkiyyar akan yadda wanna farmakin zai iya haidar da komawar 'yan ta'adda a Siriya.