Feb 06, 2018 12:41 UTC
  • Palasdinu: Hamas Ta Dauki Alhakin Kashe Wani Dan Sahayoniya

Bangaren Soja na kungiyar Hamas, wato rundunar Izzudin Kassam ne ya sanar da kashe dan sahayoniya a garin Nabulus da ke yammacin kogin Jordan.

Tashar talabijin ta 10 ta haramtacciyar Kasar Isra'ila ta bada labari a jiya litinin cewa; Wani dan share wuri zauna a yankin Selfit da ke Nablus, ya halaka bayan da aka kai masa hari da wuka.

Tuni sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra'ila suka bazu domin gano wanda ya kai hari.

A wani gefen, tashar talabijin din al-Manar ta Lebanon ya ce; 'yan sahayoniya sun mika gawar shahi Ahmad Nasar Jarrar ga iyalansa a palasdinu,

A yau talata ne dai yan sahayoniyar suka harbe Ahmad Jarrar a garin Jenin da hakan ya kai shi ga yin shahada.

Tags