Feb 09, 2018 15:48 UTC
  • Kurdawa Na Tsare Da 'Yan Ta'addan Birtaniya Biyu A Siriya

Myakan Kurdawa a Siriya sun ce suna tsare da wasu 'yan ta'addan kungiyar (IS) 'yan asalin kasar Birtaniya biyu, wadanda sanannu ne wajen azabtarwa da kuma hille kai.

Mutanen biyu mambobi ne a wani gungun 'yan ta'adda hudu duk haifafun birnin Landan, wadanda ke da hannu a garkuwa da kuma yanka turawa kimanin 27 bayan garkuwa dasu.

Daga cikinsu da akwai 'yan jaridar nan na Amurka James Foley da Steven Sotloff da kuma wasu ma'aikatan agaji na Birtaniya David Haines da Alan Henning duk dai wadanda 'yan ta'addan suka hallaka bayan garkuwa dasu.

Har yanzu dai babu masaniya akan makomar mayakan biyu da Kurdawa ke tsare da a Siriya, amma a cewar labarin akwai yiwuwar a tisa keyarsu zuwa Amurka don yi musu shari'a ko kuma a tura su gidan yarin Guantanamo Bay.

Saidai tuni wasu kungiyoyi suka fara kiran da a wa mutanen biyu shari'a mai adalci.

Tags