An Kame Mayakan Gwagwarmayar Palastinawa Na Jihadi-Islami
Hukumomin Haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi awan gaba da mayakan kungiyar gwagwarmayar Palastinawa na Jihadil-Islami guda shida.
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto cibiyar leken asiri da tsaron cikin gida na haramtacciyar kasar Siriya wato Shabak na cewa a wannan lahadi ta kame wasu mayakan kungiyar gwagwarmayar Palastinawa na Jihadil-Islami guda shida bisa zargin yunkurin hallaka Avigdor Lieberman ministan yakin Haramtacciyar kasar.
A cikin sanarwar da ma'aikatar Shabak ta fitar ta hanyar kafafen yada labaran HKI ta ce da taimakon jami'an 'yan sanda da sojoji, daga karshe mun cabke mayakan kungiyar gwagwarmyar Palastinawa na jihadil-islami guda 6 da suka sanya Bam a hanyar da ministan yakin Isra'ilan yake ficewa.
Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da mayar da martani da kungiyar Gwagwarmayar Jihadil-Islamin ta fitar.
Hukumomin haramtacciyar kasar Isra'ilan na kirkiro wasu kareraki tare da kame al'ummar Palastinu domin sanya tsoro da fargaba a cikin zukatan al'umma da a tunanisu hanan zai karya lagon gwagwarmaya, su kuma su ci gaba da mamaya yankunan na Palastinawa.