Hasan Nasrullah:Makiya Na Bayan Makarkashiya Ga Gwagwarmaya
(last modified Sat, 24 Feb 2018 19:01:14 GMT )
Feb 24, 2018 19:01 UTC
  • Hasan Nasrullah:Makiya Na Bayan Makarkashiya Ga Gwagwarmaya

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lobnon ya yi ishara kan kashin da Amirka da kawanta suke sha a yankin\, inda ya ce a yau, lokaci ya yi na raba abinda muka girba, kuma mahiman nasarorin da muka samu shi ne goyon bayan gwagwarmaya a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Tasnin na kasar Iran ya nakalto Sayyid Hasan Nasrullah, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lobnon cikin wani jawabi da ya gabatar  wannan asabar a garin Ba'alabak na gabashin kasar ya ce bayan kashin da Amirka da kawayenta da kuma kungiyar ISIS suka sha a yanki, makiya  na bayan kullawa gwagwarmaya makarkashiya ne.

Yayin da yake ishara kan ziyarar da Saktaren harakokin wajen Amirka ke kokarin kaiwa kasar ta Labnon, Sayyid Hasan Nasrullah ya ce lokacin da Rex W. Tillerson ya kama hanyar Bairout, kamata ya yi ya ce manufa Na na wannan bulago, bai kawai abinda ya shafi matsalar iyakar ruwa ba, saidai yadda za a kalubalanci kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah.

Sayyid Nasrullah ya kara da cewa in ban hukumomin Isra'ila na tsoro a yau ba, da sun ja bututun man daya yanki na tara sun kuma mamaye Man Al'ummar kasar labnon.

Har ila yau, Sayyid Nasrullah ya bukaci kawayen kungiyar Hizbullah da su goyi bayan gwagwarmaya wajen tunkarar makircin makiya na ciki da wajen kasar.

Kafin hakan dai, Ministan yakin HKI ya yi da'awar cewa babban rijiyar man fetur da iskar gaz na yanki na tare, mallakar Isra'ila ne.