Siriya : Har Yanzu 'Yan Agaji Basu Shiga Yankin Gabashin Ghouta Ba
Mar 01, 2018 10:38 UTC
Bayanai daga Siriya na cewa har yanzu ba'a samu damar da shigar da kayan agaji ba a yankin gabashin Ghoutta inda dubban fararen hula ke bukatar agaji gaggawa.
Kungiyar dake sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama ta (OSDH), ta ce duk da kwarya kwaryar tsagaita wutar da aka ayyana a yankin, babu ayarin motocin agaji da ya shiga yankin.
Rahotanni daga yankin na cewa an samu dan tsukuni tun bayan tsagaita wuta na sa'o'i biyar a ko wacce safiya da Rasha ta ayyana a yankin.
Amma duk da hakan an jiyo harbin manyan bindigogi na dakarun gwamnatin Siriya, a yayin da 'yan tada kayar baya dake yankin suka harba makaman roka kimanin 30.
Tags