Isra'ila : Kotu Ta Soke Shirin Korar Bakin Haure 'Yan Afrika
Kotun kolin Isra'ila ta soke shirin nan na gwamnati da ya tanadi korar dubban bakin haure 'yan Afrika da suka shiga Isra'ilar ba bisa ka'ida ba.
Kotun ta soke shirin ne na gwamnatin Benjamin Netanyahu, bisa karar da wasu kungiyoyin kare bakin haure suka shigar gabanta, inda ta baiwa gwamnatin har zuwa ranar 26 ga watan nan domin gabatar bayannan da zasu gamsar da ita kan shirin.
Shirin dai na gwamnatin Isra'ilar ya tanadi korar dubban bakin haure 'yan asalin kasashen Erytrea da kuma Sudan wadanda suka shiga Israi'lar ba bisa ka'ida ba kuma har yanzu basu kai ga mallakar takardar neman mafaka ba.
Mahukuntan yahudawan dai sun ba bakin hauren wa'adin har zuwa farkon watan Afrilu na su fice daga Isra'ilar, su koma kasarsu ta asali ko kuma wata kasa cen da ba ta nahiyar Turai ba.
Dama kafin hakan shirin dai na gwamnatin Netanyahu ya sha sosai a ciki da wajen kasar, musamman daga hukumar kula da bakin haure ta MDD (UNHCR).