Kungiyoyin Falasdinawa Sun Bukaci Tsige Shugaban Hukumar Falasdinu Daga Kan Mukaminsa
(last modified Tue, 20 Mar 2018 19:12:10 GMT )
Mar 20, 2018 19:12 UTC
  • Kungiyoyin Falasdinawa Sun Bukaci Tsige Shugaban Hukumar Falasdinu Daga Kan Mukaminsa

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun bukaci tsige shugaban hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Falasdinawa Mahmud Abbas daga kan mukaminsa.

A bayanin hadin gwiwa da kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa suka fitar sun yi Allah wadai da furucin shugaban hukumar Falasdinu Mahmud Abbas na zargin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da hannu a kokarin aiwatar da kisan gilla kan fira ministan Falasdinu Rami Hamdullah tare da bayyana furucin da cewa baya kan hanya kuma babban abin mamaki ne.

Har ila yau bayanin hadin gwiwar ya bukaci tsige Mahmud Abbas daga kan mukaminsa na shugaban hukumar Falasdinawa tare da hanzarta daukan matakin kalubalantar wannan furuci nashi da ke matsayin ra'ayinsa na kashin kansa.

A ranar Talatar da ta gabata ce aka tada bom a kan hanyar shigewar tawagar fira ministan Falasdinu Rami Hamdullahi a lokacin da ya kai ziyarar aiki zuwa yankin Zirin Gaza da ke karkashin ikon kungiyar gwagwarmaya ta Hamas.