Siriya Ta Musanta Yin Amfani Da Makamai Masu Guba
Gwamnatin Siriya ta musanta yin amfani da makamai masu guba a gabashin yankin Ghouta dake Damascus, kuma ta ce zargin da aka yi mata babu kamshin gaskiya.
Wani jami'in gwamnati Siriya ya ce, da zarar gwamnatin kasar ta cimma nasara wajen murkushe ta'addanci, sai a dinga zargin ta da laifin yin amfani da makamai masu guba.
A wani lokaci a yau Talata ne kwamitin tsaro na MDD zai duba wata bukata da AMurka ta gabatar na daukar mataki kan gwamnatin ta Siriya, bayan zargin amfani da makamai da ake mata.
Kasar Rasha ta ce wani ayarin sojojinta da ya ziyarci yankin, ya ce babu wata hujja datake nuna anyi amfani da makami mai guba a yankin.
Kafin hakan dai Amurka ta ce za ta yi gaban kanta ta hanyar daukan mataki mai tsauri, ko dai ya zamana kwamitin tsaron na MDD, ya amunce ko kuma A'a.