Sojojin Siriya Sun Tsarkake Yankin Duma_ Rasha
Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, sojojin gwamnatin Siriya sun kwace ikon Duma, gari na karshe dake hannun 'yan tada kayar baya a yankin gabashin Ghouta.
Bayanai daga yankin na cewa a yanzu haka, tutar Siriya ce ke kadawa a tsakiyar garin Duma
Kame garin Duma babbar nasara ce ga gwamnatin Siriya, wanda kuma babbar alama ce ta tsarkake yankin gabashin Ghouta daga duk wata barazana a cewar Janar Louri Evtouchenko, na Rasha.
Gidan talabijin din Rasha ya nuna hotunan wasu mazauna yankin kan tituna dauke da tutar Siriya, da kuma wasu tutocin kan gine gine.
Saidai wannan nasara ta zo ne a daidai lokacin da ake ta cacar baki da barazana kai hari daga Amurka da wasu kasashen yamma kawayenta, biyo bayan zargin gwamnatin Siriya da amfani da makami mai guba a yankin.
A nata bangare Rasha, ta ce za ta kakkabo duk wani makami mai linzami da Amurka zata harba kan Siriyar.