Turkiyya : Erdogan, Ya Kira Zaben kafin wa'adi
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya, ya yi kiran gudanar da zaben shugaban kasa gami dana 'yan majalisar dokoki na kafin wa'adi, a ranar 24 ga watan Yuni mai zuwa.
Wannan dai na zuwa ne a kasa da shekara guda da rabi kafin a je manyan zabukan kasar.
Mista Erdogan ya sanar da hakan ne yayin wani taron manema labarai a birnin Anakara, bayan ganawa da jagoran jam'iyyar MHP, Devlet Bahçeli, masu ra'ayin kishin kasa, da ya bukaci a kira zaben na kafin wa'adi a ranar Talata.
Mista Erdogan ya ce sun amunce kuma za'a gudanar da manyan zabukan ne a ranar Lahadi 24 ga watan Yunin 2018, kuma nan take kwamitin koli na shirya zabukan kasar zai fara shirye shiryen zabukan.
Wannan matakin dai ya zo wa da jama'ar kasar da dama da ''ba zata'' kasancewar an shafe makwanni da dama ana ta rade raden cewa za'a kira zaben amma ana musuntawa.