Saudiyya : An Bude Kofofin Sinimar Farko Ga Jama'a
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i30148-saudiyya_an_bude_kofofin_sinimar_farko_ga_jama'a
A Saudiyya, a karon farko cikin shekaru 35, 'yan kasar sun samu shiga gidan kallon Sinima a birnin Riyad, inda aka haska film din farko na Amurka "Black Panther".
(last modified 2018-08-22T07:01:44+00:00 )
Apr 21, 2018 06:41 UTC
  • Saudiyya : An Bude Kofofin Sinimar Farko Ga Jama'a

A Saudiyya, a karon farko cikin shekaru 35, 'yan kasar sun samu shiga gidan kallon Sinima a birnin Riyad, inda aka haska film din farko na Amurka "Black Panther".

Wakilin kamfanin dilancin labaren AFP, ya ce jama'ar kasar da dama ne mata da maza suka hallara a gidan sinimar a jiya Juma'a, bayan da aka yi gwajin farko a ranar Laraba data gabata.

Bayyanai sun ce nan gaba a wattani masu zuwa za'a bude wasu kofofin gidajen sinamar, wannan kasa tun bayan rufesu a shekara 1980.

Wannan dai dai shi ne share fagen bude wadansu gidajen sinima ne kusan 100 a fadin kasar nan da shekarar 2030, dake cikin manufofin matashin yarima mai jiran gado na masarautar ta Saudiyya, Mohamed Ben Salman.