Isra'ila Ta Soke Shirin Tisa Keyar Masu Neman Mafaka Na Afrika
Apr 25, 2018 10:56 UTC
Gwamnatin yahudawa 'yan mamaya na Isra'ila ta soke kudurin ta, na korar dubban masu neman mafaka 'yan kasashen Afirka.
Mai yiwuwa ne maimakon korarsu ta ci gaba da tsare su a gidajen yari na musamman da aka tanada.
Wannan mataki dai ya biyo bayan umarnin kotun koli Isra'ilar, wanda ya hana mahukunta aiwatar da korar masu neman mafakar.
Gwamnatin Benjamin Netanyahu na son korar bakin hauren galibi na kasashen Sudan da Eritrea kusan 42,000 wadanda da daman su a cewarta ke zaune a yankunan marasa galihu dake kudancin birnin Tel Aviv.
Tags