Harin Kungiyar Ashabab Yayi Sanadiyar Rufe Makarantu A Kenya
(last modified Thu, 03 May 2018 11:51:27 GMT )
May 03, 2018 11:51 UTC
  • Harin Kungiyar Ashabab Yayi Sanadiyar Rufe Makarantu A Kenya

Hare-haren da kungiyar ta'addancin ta Ashabab ke kaiwa arewa maso gabashin kasar kenya ya sanya malimam makaranta da damu gudu daga yankin.

Kimanin maliman makaranta 120 ne a garin Mandera dake arewa maso gabashin kasar Kenya suka gudu, sanadiyar hare-haren ta'addancin da mayakan Ashabab ke kaiwa yankin, lamarin da ya yi sanadiyar rufe makarantun gwamnati da dama a yankin,

Kimanin makarantun Piramire 224 da na Sakandere 42 ne aka rufe a garin Wajir dake tsakiyar jahar arewa maso gabashin kasar  sakamakon gudun da maliman makarantar suka yi daga yankin.

Harin baya-bayan nan da kungiyar Ashabab din ta kai garin na Wajir a ranar 16 ga watan Avrilun da ya gabata ya yi sanadiyar mutuwar maliman makaranta guda biyu.

A shekarar 2011 ne mayakan na Ashabab suka fara kai hare-hare ba kakkautawa a cibioyin harakokin ilimi na kasar ta Kenya.