Gaza : Akalla Falasdinawa 55 SuKa Yi Shahada
Sojojin yahudawa sahayoniya sun kashe falasdinawa akalla 55 a zirin Gaza, a zanga zanga da falastinawan ke yi kan mayar da Kudus babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Ko baya ga wadanda sukayi shahada da akwai wasu kimanin dubu guda da suka samu raunaka a cewar mahukuntan Falasdinu.
Lamarin ya zo ne a yayin da Amurka ke bude ofishin jakdancinta a birnin na Kudus, a jiya Litini, duk da shawarwarin da aka bata kan irin bannar da za ta haifar matukar ta ayyana Kudus din a matsayin babban birnin Isra'ilar.
Wannan dai ya sa adadin Falasdiwa da sukayi shahada tun daga soma wannan boren a ranar 30 ga watan Maris da ya gabata zuwa 109.
Ana dai ganin adadin zai iya karuwa, a yayin da ake tunkarar zagayowar ranar ''Nakba'' ma'ana Balaki'' ranar da kafa Is'raila kenan a shekara 1948 wacce ta yi sanadin raba daruruwan iyalen Falasdinawa da matsugunnansu.