Ma'aikatar Kudi Ta Amurka Ta Dorawa Shuwagabannin Hizbullah Takunkumi
(last modified Fri, 18 May 2018 06:29:13 GMT )
May 18, 2018 06:29 UTC
  • Ma'aikatar Kudi Ta Amurka Ta Dorawa Shuwagabannin Hizbullah Takunkumi

Ma'aikatar kudi ta kasar Amurka ta bada sanarwan kakabawa shuwagabanni da wasu kamfaninin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Takunkumi.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar ma'aikatar kudin tana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa takunkumin ta hada da shugaban kungiyar ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasarral, da mataimakinsa Sheikh Naeem Kasim. Sauran kuma sun hada da Husain Khalil, mai bawa shugaban kungiyar shawara kan al-amuran siyasa, Ibrahim Amin Assayyeed shugaban majalisar siyasa ta kungiyar, Muhammad yazbak shugaban harkokin shari'a na kungiyar. Sai kuma wasu kamfanini guda biyar, wadanda ma'aikatar ta ce suna da danganataka da kungiyar.

Ma'aikatar da bayya cewa ta dau wannan matakin ne don kungiyar ta Hizbullah kungiya ce ta yan ta'adda wacce kuma take tallafawa yan ta'adda a kasashen duniya da dama. 

Gwamnatin Amurka dai ta dau wannan matakin ne bayan da gamayyar jam'iyyu masu goyon bayan kungiyar Hizbullah suka sami gagarumar nasara a zaben majalisar dokokin da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu da muke ciki a kasar  ta Lebanon. 

Banda haka kungiyar Hizbullah tana kan gaba a cikin gamayyar kasashe da kungiyoyi masu yakar kungiyoyin yan ta'adda a kasar Leban da sauran kasashen yankin wadanda suke samun goyon bayan Amurka da kuma Saudia da kawayenta.