An Yi Gargadi Kan Tasirin Gwamnatin H.K. Isra'ila A Nahiyar Afrika
(last modified Sat, 19 May 2018 12:00:00 GMT )
May 19, 2018 12:00 UTC
  • An Yi Gargadi Kan Tasirin Gwamnatin H.K. Isra'ila A Nahiyar Afrika

Wani dan jarida kuma tsohon dan Majalisar Dokoki a kasar Tunusiya ya yi gargadi kan tasirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a nahiyar Afrika.

A ganawarsa da jaridar Al-Ahad: Hashim Al-Hajji ya ce a halin yanzu haka gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tana ci gaba da yin kutse a nahiyar Afrika tare da tasiri kan harkokin siyasar kasashen da nufin samun damar cimma munanan manufofi a nahiyar.

Al-Hajji ya kara da cewa: A halin yanzu haka babu wani gagarumin shiri da kungiyoyin fararen hula a kasashen Larabawa da na Musulmi suke yi domin kalubalantar bakar siyasar haramtacciyar kasar Isra'ila lamarin da zai bada dama ga shugabannin kasashen mika kai ga haramtacciyar kasar Isra'ila tare da yin watsi da matsalar Palasdinu.