Palasdinu Ta Bukaci ICC Ta Binciki Isra'ila Kan Laifukan Yaki
Ministan harkokin wajen Palasdinu, Riyad al-Maliki, ya bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, data bude binciken gaggawa kan laifukan yaki da wariyar launin fata da ake zargin aikata wa kan Palasdinawa.
Wannan bayyanin ya fito ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Palasdinun ya yi da mai shigar da kara ta kotun ta ICC, Fatou Bensouda, cibiyar kotun dake a birnin la Haye.
Mista Al-Maliki, ya shaida wa manema labari cewa, wannan mataki ne mai matukar mahimmanci da tarihi wajen yi wa al'ummar Palasdinu shari'a kan ukubar da suke ci gaba da fuskanta, don gurfanar da wadanda suke da hannu a ciki.
A cewar Al'Maliki, matakin ya biyo bayan tsanantar kisan da ake wa al'amarin ta na Palasdinu da yadda lamarin ke kara kamari musamman yadda ake harbe masu zanga zangar lumana a zirin Gaza.
A ranar 14 ga wata nan na Mayu, a daidai lokacin da Amurka ke bikin mayar da ofishin jakadancinta a birnin Qudus, Palasdinawa 62 ne suka yi shahada a lokacin da suke zanga zangar neman hakkokinsu, sakamakon harbin bindiga daga sojojin yahudawa 'yan kama wuri zauna na Isra'ila.