Saudiyya : Al'Qaida Ta Ce Sauye-sauyen Bin Salman, Aikata ''Zunubi Ne''
(last modified Fri, 01 Jun 2018 14:49:32 GMT )
Jun 01, 2018 14:49 UTC
  • Saudiyya : Al'Qaida Ta Ce Sauye-sauyen Bin Salman, Aikata ''Zunubi Ne''

Kungiyar 'yan ta'adda ta Al'Qaida a kasashen Larabawa, ta ce sabbin sauye-sauyen zamantakewa na yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohamed Ben Salma, aikata zunubi ne.

A sanarwar da reshen kungiyar a kasashen Larabawa na Amaq ya fitar, ya ce sabbin sauye-sauyen matashin yariman, tamakar aikata zunubi su ke, inda kungiyar ta bada misalin cewa, san sauya wuraren ibada wato masallatai da gidajen kallon sinima a Saudiyyar.

Kungiyar ta Aqpa, ta kuma ce, manufofin yariman sun kai har ga canza litafen manyan malamai da abubuwan shirme da wasu matakai da ba zasu haifar da komai ba, illah bude kofar cin hanci da rashawa.

Kungiyar dake ikirari da sunan jihadi ta bada misali kuma da wasan dambe farko da aka yi a birnin Jeddah a karshen watan Afrilu, inda ta ce 'yan wasan kasashen kafirai suka yi wasa cikin tufafi masu nuna tsiraici gaban matasa musulmai mata da maza.

A shekarar data wuce ne hukumomin na Saudiyya suka dau matakin shigar da harkoki nishadi a kasar, a matsayin wani muhimmin mataki na bunkasa kasar nan da shekara ta 2030, mai taken ''Vision 2030''.