Iraki : An Zartar Da Hukuncin Kisa Ga 'Yan Ta'adda 12
(last modified Fri, 29 Jun 2018 15:01:09 GMT )
Jun 29, 2018 15:01 UTC
  • Iraki : An Zartar Da Hukuncin Kisa Ga 'Yan Ta'adda 12

Hukumomi a Iraki sun sanar da cewa an zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane 12, da ake zargi da alaka da ayyukan ta'addanci, bisa umurnin Fira ministan kasar Haider al-Abadi.

A jiya Alhamis ne dai fira ministan kasar, Haidar al-Abadi, ya bada umurnin zartar da hukuncin kisa kan wasu daruruwan 'yan ta'adda da aka yanke wa hukucin kisa, ciki har da mata da wasu 'yan kasashen waje.

Sanarwar dai bata fayyace ko 'yan asalin wacce kasa ne ba, aka zartar wa da hukuncin.

Hukuncin dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan gano gawawakin wasu 'yan kasar Irakin takwas da kungiyar 'yan ta'adda ta (IS), ta yi garkuwa dasu, wadanda kuma wani faifan bidiyo data fitar ya yi barazanar kashesu idan gwamnatin Bagadaza bata sallami matan data danganta da 'yan jihadi ba.