Iran Ta Gargadi Saudiyya Kan Kara Yawan Man Fetur
Teheran, ta gargadi mahukuntan Riyad, akan yunkurin kara yawan man fetur din da Saudiyyar ke hako wa.
Wakilin Jamhuriya Musulinci ta Iran, a kungiyar kasashe masu arzikin man fetir ta OPEC ne, Hossein Kazempour Ardabili, ne ya yi wannan gargadin ga Saudiyya.
Mista Kazempour, ya ci gaba da cewa, muddin Saudiyyar ta kara adadin man fetur din da aka kayyade mambobin kungiyar, zasu hako , to ko akwai yiwuwar a kira wani taron gaggawa na kungiyar ta OPEC, domin tattauna batun.
A don haka ya bukaci Saudiyya, data mutunta yarjejeniyar da aka cimma a kungiyar, na kayyade yawan man da ko wacce mamba zata hako wa.
Saudiyya dai bata da hurimin kara yawan man fetur dinda take fitar wa, na ganga Miliyan 10,06 kamar yadda yarjejeniyar da kasashe mambobin kungiyar suka cimma ta kayyade mata.