Siriya : 'Yan Gudun Hijira Deraa Sun Fara Komawa Muhallansu
A Siriya, dubban 'yan gudun hijira ne da suka kaurace wa muhallansu suka fara komawa gida, bayan sanar da cimma yarjejeniya tsakanin gwamnati da 'yan tada kayar baya dake a yankin Deraa dake kudancin kasar.
Da yammacin jiya Juma'a ne, bangarorin suka sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, a shiga tsakanin kasar Rasha, bayan shafe makwanni biyu na farmakin da dakarun gwamnatin Siriya suka kaddamar na kwato yankin daga hannun 'yan tada kayar bayan dake yankin na Deraa.
A bisa yarjejeniyar dai, ma'aikatun gwamnati a yankin zasu koma bakin aiki a yankin, a yayin da gwamnatin Siriya zata karbi daukacin ikon wuraren da 'yan tada kayar bayar ke rike da akan iyaka da kasar Jordan, kamar yadda kamfanin dilancin labaren Siriyar na Sana ya rawaito.
Alkalumman da MDD, ta fitar sun nuna cewa kimanin mutane 325,000 ne suka bar muhallansu tun bayan da sojojin gwamnatin Siriyar suka kaddamar da harin na kwato birnin daga hannun tsagerun a ranar 19 ga watan Yuni da ya gabata.