Turkiyya : An Kori Ma'aikata Sama Da 18,000
(last modified Sun, 08 Jul 2018 15:43:53 GMT )
Jul 08, 2018 15:43 UTC
  • Turkiyya : An Kori Ma'aikata Sama Da 18,000

Gwamnatin Turkiyya ta sanar da korar ma'aikata sama da 18,000 daga bakin aiki, wadanda mafi yawa daga cikinsu ma'aikatan tsaro ne.

Daga cikin wadanda kudirin dokar ya shafa da yawansu ya kai 18.632, akwai 'yan sanda sama da dubu tara, da sojoji dubu shida, da aka kora, kamar yadda wata jaridar gwamnatin kasar ta sanar a yau.

Daga bangaren ma'aikatar shari'a ma akwai mutun kimanin 1000, sannan a ma'aikatar ilimi mutun 650 da dukanninsu aka tabbatar da korarsu daga bakin aiki.

Ana dai kallon wannan kudirin doka, da cewa shi ne irinsa na karshe da aka taba dauka a karkashin dokar ta baci da ake ta sabunta wa a kasar, tun bayan yunkurin juyin mulkin kasar da bai yi nasara ba a watan Yuli na shekara 2016 data gabata.

Kafofin yada labarai a Turkiyyar sun rawaito cewa, a gobe Litini ce, ake sa ran dage dokar ta bacin da aka kafa tun waccen lokacin a kasar, bayan bikin rantsar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan, a wani wa'adin mulki, wanda dama daya ne daga cikin al'kawuran da ya yi a yakin neman zabensa.