Majalisar Dokokin HKI Ta Amince Da Dokar Wariya A Kasar
Majalisar dokokin HKI wacce ake kira Knesset ta amince da wata doka wacce ta tabbatar da wariya tsakanin mazauna haramtacciyar kasar, inda ta amince da yahudawa kadai a matsayin yan kasa.
Bayan amincewa da wannan dokar ta wariya kungiyar kasashen larabawa ta yi allahwadai da dokar ta kuma bukaci kasashen duniya su tashi don sauke wajibin da ya hau kansu na hana dokar wariya da nuna bambanci wacce majalisar Knesset ta amince da ita a jiya Alhamis.
Dokar dai ta yi watsi da larabawa wadanda yawansu ya kai kimani kashi 20 % na yawan mutanen da suke zaune a yankunan da HKI ta ke mamaye da su. Dokar ta tabbatar da harshen hibru a matsayin harshen da gwamnati da makarantu ta amince da yin watsi da harshen larabci, da kuma fifita yahudawa a kan duk wanda ba bayahude ba a kasar.
Wannan dokar dai ta HKI tamkar irin ta Afrika ta kudu kafin faduwar tsarin wariya a kasar