Siriya : Kurdawa Sun Amince Da Yin Shawarwari Da Gwamnati
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32562-siriya_kurdawa_sun_amince_da_yin_shawarwari_da_gwamnati
Kwamitin dimokuradiyya na Syria, na hukumar siyasa da Kurdawa suka kafa, ya ce a shirye kwamitin ya ke ya yi shawarwari tare da gwamnatin kasar Syria.
(last modified 2018-08-22T11:32:11+00:00 )
Jul 31, 2018 11:16 UTC
  • Siriya : Kurdawa Sun Amince Da Yin Shawarwari Da Gwamnati

Kwamitin dimokuradiyya na Syria, na hukumar siyasa da Kurdawa suka kafa, ya ce a shirye kwamitin ya ke ya yi shawarwari tare da gwamnatin kasar Syria.

A halin yanzu, rundunar sojojin dimokuradiyya mai adawa da gwamnati dake karkashin jagorancin dakarun Kurdawan, ta mamaye galibin yankunan dake arewa da kuma gabashin kasar.

A ranar 26 ga watan nan ne akayi shawarwari tsakanin bangarorin kan tattauna batun yankunan da dakarun Kurdawan suka mamaye a arewa da kuma gabashin kasar karo na farko.