Palasdinawa Sun Shigar Da Karar Gwamnatin H.K.Isra'ila A Gaban Kotun ICC
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32585-palasdinawa_sun_shigar_da_karar_gwamnatin_h.k.isra'ila_a_gaban_kotun_icc
Kwamitin shirya zanga-zangar lumana kan neman hakkokin Palasdinawa ya sanar da cewa: Kwamitin ya shigar da karar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a gaban kotun kasa da kasa da ke shari'ar manyan laifuka a duniya ta ICC
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Aug 02, 2018 02:54 UTC
  • Palasdinawa Sun Shigar Da Karar Gwamnatin H.K.Isra'ila A Gaban Kotun ICC

Kwamitin shirya zanga-zangar lumana kan neman hakkokin Palasdinawa ya sanar da cewa: Kwamitin ya shigar da karar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a gaban kotun kasa da kasa da ke shari'ar manyan laifuka a duniya ta ICC

Kwamitin shirya zanga-zangar lumana kan neman hakkokin Palasdinawa musamman hakkin 'yan gudun hijirar Palasdinu na dawowa muhallinsu da bukatar kawo karshen killace yankin Zirin Gaza, ya gabatar da cikakken rahoto ga kotun kasa da kasa da ke shari'ar manyan laifuka a duniya ta ICC kan irin matakan wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila take dauka kan al'ummar Palasdinu a lokacin gudanar da zanga-zangar lumana.

Kwamitin ya kara da cewa: A rahoton da ya gabatarwa kotun kasa da kasar ta ICC ya fayyace cewa: Palasdinawa fiye da 150 ne sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kashe a zanga-zangar lumanar, kamar yadda wasu fiye da 16,000 suka samu raunuka.

Tun a ranar 30 ga watan Maris na wannan shekara ce al'ummar Palasdinu suka fara gudanar da zanga-zangar lumana a matsayin ranar kasa domin neman hakkinsu na dawowar 'yan gudun hijirar Palasdinawa kasarsu ta gado tare da kawo karshen killace yankin ZIrin Gaza da ya yi sanadiyyar wurga al'ummar yankin cikin mummunan hali.